A ci gaba da tattaunawar da ake yi tsakanin masu garkuwa da dalibai mata guda shida tare da mataimakin shugaban makarantarsu da wadansu ma’aikata biyu na Kwalejin Engravers dake Kakau Daji a karamar hukumar Chikun domin ganin an sake su, masu garkuwa da mutanen sun sake neman sai an biya su naira miliyan 80 a maimaikon miliyan 50 da suka nema kafin su saki daliban da suka yi garkuwa da su.
Inda suka tabbatar da cewa yanzu sun fasa karbar dunkulallen kudi domin sakin su, dole ne kowanne Iyaye su biya Naira miliyan 10 ga duk mutum daya da suka kama kafin su sake su.
A ranar Alhamis aka sace daliban da misalin karfe 12:10 na dare. A wata hira da aka yi da daya daga cikin masu tattaunawa da masu garkuwa da mutanen domin ganin an sake su, ya tabbatar da cewa ‘yan bindigar sun yi watsi da bukatar farko inda suka tsaurara matakai yanzu.
Gwamnatin jihar Kaduna dai ta ce tana iya bakin kokarinta wajen ganin ta ‘yanto wadanda aka sace din.