Rahotanni sun bayyana cewa an sako Dalibai biyu da aka sace a makarantar haɗaka ta Glory Land da ke Igarra, karamar hukumar Akoko-Edo ta Edo, bayan an biya su kudin fansa Naira miliyan 6.
Wata ‘yan uwa a ɓangaren mutanan ta bayyana cewa an sako ‘yan matan biyu ne da yammacin ranar Juma’a bayan an biya su kudin fansa domin a sake su.
DUBA WANNAN LABARIN: IGP ya bukaci a miƙa sunayen ‘yan sandan dake aikin zaben jihar Anambra
Majiyar ta ce, “Ina iya tabbatar muku da cewa an sako ‘yan matan ne bayan an biya Naira miliyan 6. Sun koma cikin dangi kuma mun yi farin cikin dawowar su.”
Idan dai za a iya tunawa wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da daliban makarantar Glory Land a ranar Talata da misalin karfe 5.35 na yamma a kan titin Igarra-Auchi, kusa da Ikpeshi, karamar hukumar Akoko Edo a jihar Edo.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Edo, SP Kontongs Bello wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce tuni jami’an ‘yan sanda da sojoji da ’yan banga sun bazama daji a kokarin ceto yaran da aka sace.
Comments 1