By Abbas Yakubu Yaura
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ASP Mohammed Jalige, ya shaida wa manema labarai ranar Lahadi a Zariya cewa an sako ma’aikatan da aka yi garkuwa dasu a ranar Asabar, inda ya kara da cewa ana kokarin ganin an sako sauran ukun da aka yi garkuwa dasu.
Sai dai jami’in hulda da jama’ar ya ki cewa komai kan ko an biya kudin fansa ne kafin a sako ma’aikatan da aka sace ko ba’a biya ba.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa a ranar 8 ga watan Nuwamba, Misis Deborah Mugu, Daraktan ilimi da ci gaban jama’a, da mataimakinta, Dalhatu Aliyu-Awai, da wasu ma’aikatan karamar hukumar Zaria su 11 ne ‘yan bindiga suka sace.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa An yi garkuwa da ma’aikatan ne a garin Kidandan da ke karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna, a hanyarsu ta zuwa ta aziyya ga wani ma’aikacin mai suna Dogara Abdullahi bisa rasuwar mahaifinsa.
Sai dai wata majiya mai tushe data nemi a sakaya sunanta ta shaida wa NAN cewa an sako ma’aikatan ne bayan an biya masu garkuwa da mutanen kudin fansa Naira miliyan 40.
Ya kara da cewa ‘yan uwan wadanda abin ya shafa sun bada gudummawar kudi domin biyan kudin fansa, ya kara da cewa masu garkuwa da mutanen ba su saki uku daga cikin ma’aikatan da aka sace ba saboda wasu sharudda na sakin Naira miliyan 40 da kuma sabbin babura guda uku.
Da aka tuntubi shugaban karamar hukumar Zariya, Alhaji Aliyu Ibrahim, ya ce ba zai iya kara wani abu a cikin abin da majiyar iyalan ta shaida wa NAN.
Sai dai Da aka ci gaba da tambayar sa ko majalisar zata samar da sabon baburan ga masu garkuwar domin a sako sauran ma’aikatan nasu uku, Ibrahim yace: “Ku koma majiyarmu”.