Kimanin mutane 65 na cocin Baptist da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Kaduna an sako su daga hannun wadan da suka yi garkuwa da su.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da su ne a ranar 31 ga watan Oktoba a lokacin da suka kai hari cocin Emmanuel Baptist da ke Kakau Daji a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna. Sai dai sun kashe mutum biyu daga cikin wadan da aka kama bayan ‘yan kwanaki.
Gidan talabijin na Channels ya bada rahoton cewa, A ranar Asabar ne aka kawo wadan da abun ya shafa da suka hada da mata da maza da kananan yara zuwa cocin Albarkar Baptist da ke babban birnin jihar Kaduna bayan an sallame su kuma aka sada su da iyalansu.
Wani dan uwan daya daga cikin wadan da harin ya rutsa da su ya shaidawa gidan talabijin na Channels cewa sun biya kudin fansa domin a sako su.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya ce sojoji sun mika wadan da lamarin ya shafa ga gwamnatin jihar domin cigaba da ganawa da iyalansu.
Ya kuma kara da cewa, bayan an sallame su, sojoji sun kai su asibiti domin a duba lafiyarsu.