By Abbas Yakubu Yaura
Rahotanni sun bayyana cewa an sako Basaraken gargajiyar da aka yi garkuwa da shi a Jihar Filato, Charles Mato Dakat.
An yi garkuwa da Dakat wanda shi ne basarake a masarautar Gindiri a karamar hukumar Mangu a jihar lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari fadarsa a ranar Lahadin da ta gabata da misalin karfe 1 na dare.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Wadanda suka yi garkuwa da shi sun tuntubar ‘yan uwa bayan ‘yan kwanaki inda suka bukaci a biya su kudin fansa kimanin naira miliyan 500 kafin su sako sarkin.
Sai dai an tattaro cewa daga karshe basaraken ya sake samun ‘yancinsa da sanyin safiyar Juma’a.
Wata majiya mai tushe ta tabbatar da sakin Dakat ga Jaridar PUNCH a Jos ranar Juma’a.
Ya ce: “Allah ya karbi addu’o’inmu. An saki Mai Martaba Sarki Charles Mato Dakat. Yana cikin koshin lafiya.
Sai dai kuma da aka tambaye ta ko nawa aka biya masu garkuwa da mutane domin a sako sarkin, majiyar ta ce, “Abin da zan iya fada muku shi ne rayuwa ta fi kudi. Na gode da addu’o’in ku, ƙarfafawa da goyon baya. Godiya ta tabbata ga Allah, manyan abubuwan da ya yi kuma zai ci gaba da yi.”
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, Ubah Ogaba, da aka tuntube shi, ya ce zai koma ga wakilinmu kan lamarin amma har yanzu bai yi bayanin hakan ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.