By Abbas Yakubu Yaura
Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, a ranar Talata, an bayyana cewa sun tare hanyar Abuja zuwa Kaduna tare da yin garkuwa da wasu matafiya.
Daya daga cikin matafiyan, Alhaji Ibrahim Musa ya shaidawa Jaridar DAILY POST cewa da kyar ya tsallake rijiya da baya daga harin.
Ya ce an dauki sama da awa daya suna gudanar da atisayen.
A cewarsa, suna zuwa Kurmin Kare, kusa da Katari, kwatsam sai ya fara jin karar harbe-harbe.
“Zan je Abuja ne domin in ziyarci wani abokina da ya yi mini alkawarin ba ni kwangila. Tsakanin Kurmin Kare, na fara jin karar harbe-harbe, amma ban san alkibla ba. Sai na yi ƙarfin hali na motsa, amma a wannan karon, ina tuƙi a hankali don in sami alkiblar da ake harbe-harben.
“Bayan zuwa mahadar, kusa da Katari, na ga motoci da yawa sunyi cirko cirko, sai na juya dan na tsere,” inji shi.
“Ya ce yayin da ya ke komawa Kaduna na ga ayarin jami’an tsaro, amma ‘yan fashin sun tafi da wadanda abin ya shafa zuwa cikin daji.
Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ta hannun ofishin hulda da jama’a na ‘yan sandan, ASP Mohammed Jalige, bai amsa kiran da aka yi masa domin tabbatar da faruwar lamarin ba.