• Yan bindigan da suka yi garkuwa da daban Kwalejin Nuhu Bamalli dake Zaria sun bukaci naira Milliyan 22 da dubu dari biyar a matsayin Kudin fansa.
• Tun da fari dai naira milliyan 10 suka fara bukata daga hannun iyalan wadanda aka sace, kafin su dawo dashi naira milliyan biyu da budu dari biyar ga kowani mutun daya.
• Hukumomin Kwalejin since an Sanya jami’an tsaro domin kaucewa afkuwan hakan a nan gaba.
Yan bindigan da suka yi garkuwa da daliban Kwalejin kimiyya da fasaha ta Nuhu Bamalli dake Zaria na jihar Kaduna, a makonni biyu da suka gabata, sun bukaci naira milliyan 22 da dubu dari biyar, a matsayin kudin fansa.
KARANTA WANNAN LABARAN: Rundunar yan sanda ta kashe wasu da take zargin tada kayar baya ne.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, Masu Garkuwan, sun tuntubi wasu daga cikin iyalan Dalibai 7 da Malamai 2 da akayi garkuwa dasu, inda suka bukaci naira milliyan 2 da dubu dari biyar, a matsayin kudin fansa,.ga kowani mutun daya, da a kayi garkuwa dashi.
Wata na kusa daga cikin daliban da a kayi garkuwa dasu din ce, ta fadawa wakilin jaridar Daily Trust cewa, ” Tun da fari masu Garkuwa da mutanan sun bukaci naira milliyan goma ne, ga kowani mutun, kafin daga bisani su sassauta kudin, zuwa naira milliyan 2 da dubu dari biyar, a matsayin kudin fansan kowan nan su”. Inji ta.
Ta kuma kara ce, Dalibai biyu daga cikin wadanda akayi garkuwa dasun mata ne, inda bayan tattaunawa da masu garkuwa da mutanan, sunyi alkawarin sakin matan batare da biyan ko si-si ba, wanda haryanzu kuma basu cika alkawarin da suka dauka ba.
Ta ce “Da aka tambaye masu Garkuwan danga ne da lafiyar matar auren dake cikin wadanda suke tsare a hannun su, sun ce wannan ba matsala bane, kuma zasu iya sakin su, idan hali ya bada dama” inji matar
Idan za’ iya tunawa dai, Mahukunta makarantar, sun tabbatar wa Malamai da Dalibai cewa, An ruga da sun sanya jami’an tsaro a ciki, da wajen makarantar, inda Kuma tuni aka fara aikin katange makarantar baki daya, domin guje wa harin yan bindiga.