‘Yan bindiga sun kashe wani da sukayi garkuwa da shi bayan sun karbi Naira miliyan 1 daga hannun iyalansa, inji rahoton Daily Trust.
A watan Fabrairu, Daily Trust ta ruwaito cewa ‘yan bindigar sun kai farmaki gidan mamacin da ke Rigachikun a karamar hukumar Igabi inda suka yi awon gaba da shi tare da wasu a yankin ciki har da wata amarya.
A lokacin farmakin, an harbe wani jami’in kwastam da ke aiki da sashin kula da ayyuka na tarayya (FOU) Zone B shiyar Kaduna, inda daga bisani ya mutu a asibiti.
Wata mata a yankin ta shaida wa jaridar Daily Trust labarin rasuwar, inda tace lamarin ya afku ne a daren ranar Talata bayan da ‘yan uwansa suka kai wa ‘yan fashin kudin fansa.
“Sun harbe shi ne bayan karbar kudin fansa da aka Kai musu. Duk mazauna yankin sun kadu bayan da suka samu labarin rasuwarsa,” inji ta.
Daily trust ta ruwaito cewa an binne mamacin ne a unguwar Unguwar Shanu inda iyalansa ke zaune. An kuma bayyana cewa har yanzu amaryar da wani mutum guda na tare da wadanda suka yi garkuwa da su