Daga: Abbas Yakubu Yaura
An yi garkuwa da wasu ‘yan wasan kwallon kafa na Najeriya mata guda 6 a kauyen Oronigbe da ke jihar Edo, kan iyaka tsakanin jihohin Delta da Edo.
An tattaro cewa an sace ‘yan matan ne da misalin karfe 6 na yammacin ranar Juma’a yayin da suke dawowa daga gasar kwallon kafa a Owa-Alero a karamar hukumar Ika ta Arewa-maso-gabas a jihar Delta.
KARANTA WANNAN LABARIN: Rikicin Ta’addanci: Tubabbun ‘Yan Boko Haram Sun Fara Tsaftace Maiduguri
Miji ga daya daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su, ya ce an kulla alaka da ‘yan uwa yayin da masu garkuwa da mutane suka bukaci Naira miliyan 5 a matsayin kudin fansa ga kowannen su.
A cewarsa, “sun je garin Owa-Alero ne domin buga wasan kwallon kafa. Don haka, a hanyarsu ta dawowa, an yi garkuwa da su a yankin Oronigbe, dake kan iyaka tsakanin Delta da jihar Edo.
“Wasu daga cikin wadanda abin ya shafa su ne Misis Precious Agbajor, wato matata, Abraham, Nancy, Beatrice ciki har da direban motar.”
“Su shida ne da ke cikin gidan masu garkuwa da mutane. An kai rahoton lamarin zuwa ga ofishin ‘yan sanda na Oronigbe.”
“Masu garkuwa da mutanen sun tuntube mu, kuma suka ce in biyawa matata Naira miliyan 5. A gaskiya, na rikice yayin da nake magana da ku yanzu. ”
Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Delta, DSP Bright Edafe, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya kara da cewa lamarin ya faru ne a jihar Edo ta Najeriya.