Masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da matan aure biyu a kauyen Piri da ke yankin Kwali a Babban birnin tarayya Abuja.
Wani mazaunin kauyen mai suna Emos Bako, ya ce, lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:22 na daren ranar Lahadi, lokacin da masu garkuwa da mutanen suka mamaye unguwar Baki daya.
Ya ce da fari sun shiga gidan da suka yi garkuwa da wata matar aure da karfi tuwo, kafin su sake farmakan wani gida a unguwar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mahara sun kashe Mutum 12 tare da jikkata 2 a Zangon Kataf
Kazalika Wani dan uwan daya daga cikin wadanda aka sace, wanda ya bukaci a sakaya sunan shi ya ce, mijin daya daga cikin wadanda abin ya rutsa da su baya gida lokacin da lamarin ya faru, ya kara da cewa, har yanzu ba a fara tuntubar masu garkuwa da mutanen ba.
A wani labarin Kuma makamancin wannan.
‘Yan bindiga sun yi wa wasu mutane kwanton bauna tare da yin garkuwa da mutum hudu a kan hanyar Ayetoro-Ekiti Otun a jihar Ekiti, wadanda abin ya rutsa da su, a cewar wasu da ba a san ko suwaye ba daga yankin, ‘yan bindigar sunyi garkuwa da su zuwa cikin daji.
Bayanai sun bayyana cewa lamarin ya shafi motocin bas guda biyu da suke dauke da fasinjoji daga Otun Ekiti, inda maharan suka yi nasarar tsare mutane hudu daga cikin fasinjojin yayin da wasu suka tsere.
Rahotanin sunce wata majiya data shaidawa manema labarai a Ado-Ekiti ranar Litinin tace daya daga cikin wadanda suka tsere ya shaida masu cewa ‘yan bindigar sun tafi da fasinjoji hudu da suka yi garkuwa dasu daga cikin motocin bas din guda biyu.
Wani abin birgewa ga abin da ya faru shi ne, wadanda ake zargin masu garkuwa da mutanen, da suka fahimci cewa sun yi asarar babban burin su, ranar Lahadi da yamma, sun fara kai hari kan masu babur na kasuwanci ta hanyar harbi ba kakkautawa ta sama don tsoratar da mutane.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Ekiti, Sunday Abutu,ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce, “ Mun ji labarin kuma mun tura jami’an mu wurin dan bin sawun masu garkuwar.
“An samu afkuwar hadarin sace mutane a safiyar yau, inda abun ya fara tun a yammacin ranar Lahadi lokacin da wasu da ake zargin ‘yan fashi ne suka kai hari kan wani mutum da ‘yan sanda suka ceto, Amma a safiyar yau, mun samu labarin cewa wadanda ake zargin sune suka sace wasu masu bin hanya, ‘Yan sanda na kan bin sawun masu garkuwar,” in ji shi.
Sai dai Koda majiyar jaridar Dimokuradiyya ta tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan birnin tarayya, ASP Daniel Y Ndiparya, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce, rundunar za ta tabbatar da cewa, an ceto mutanen da akayi garkuwa da su lami lafiya
Comments 1