By Abbas Yakubu Yaura
An fara turuwar gasar neman cike gurbin kujerar Alaafin na Oyo da akalla masu jiran gado 20 daga gidan sarautar Owoade da ke nuna sha’awarsu ta neman su gaji Oba Lamidi Adeyemi.
Iyalan masu mulki na Owoade na daya daga cikin iyalai biyu masu mulki a karkashin mulkin gidan sarautar Agunloye, a cewar Mogaji na iyalan, Yarima Adediwura Owoade.
Mogaji ya bayyana haka ne a hirarsa da wakilinmu a ranar Alhamis.
Ya ce ‘yan uwa sun bude rajista ga duk wanda ke da sha’awar gidan ya rubuta sunayensu tare da mika takardun karatunsu.
Ya ce ‘yan uwa za su gayyaci mataimakin shugaban jami’o’in da ke kusa da su domin tantance sunayen da nufin gabatar da wanda ya fi cancanta ga Oyo Mesi, wadanda su ne sarakuna.
Ya kara da cews an dade ana yaudarar dangin amma yanzu a shirye suke don ganin daya daga cikin basaraken ya hau karagar mulki.
Owoade ya ce, “kimanin Yarima 20 daga Iyalan Mulkin Owoade sun nuna sha’awarsu ta zama Alaafin na gaba. Amma kamar yadda na fada muku za mu tantance su kuma mu gabatar da mafi kyau.
“Dukkan su ‘ya’yana ne. Duk wanda ya fito takara daga gidan Owoade dana ne. Mu iyali daya ne. Mun hadu da shi haka kuma muna son ta kasance a haka.
“Ina so in jaddada wannan cewa duk wanda aka zaba daga dangin Owoade zai yi aikin ci gaban gari kuma a shirye muke mu sasanta duk wata baraka da kowa a Oyo. Muna son zaman lafiya kuma duk abin da ya zama sanadin irin wannan fada, a shirye muke mu sasanta shi. Muna son hadin kai a Oyo, muna son Oyo ta zama daya domin inganta ci gaba da tsaro”.
Kujerar ta zama ta fanko tun bayan rasuwar Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi, a ranar 22 ga watan Afrilu yana da shekaru 83.
Comments 1