Gwamnatin jihar Bauchi a ranar Juma’a ta bayyana cewa an sake samun sabbin mutum 9 da suke dauke da cutar Korona a jihar, wanda wannan ya sanya yanzu masu cutar a jihar suka kai 38.
Dr Aliyu Maigoro, Kwamishinan lafiya na jihar shi ne ya bayyanawa manema labarai hakan, inda ya ce sakamakon mutum tara din NCDC suka aiko musu a cikin daren ranar Alhamis daga Abuja.
Ya tabbatar da cewa 87 cikin 90 da suka dawo jihar daga jihohin Ribas, Inugu, an killace su a Otel din Destiny, kuma tuni aka sallame su bayan an samu ba su dauke da cutar, a yayin da mutum uku ne kawai aka samu da cutar.