Hukumar dakile cututtuka masu yaduwa ta Nijeriya, NCDC ta ce mutum 114 sun sake kamuwa da cutar korona cikin sa’a 24 da ta wuce a sassan Nijeriya, bisa wannnan, yanzu adadin wadanda suka kamu ya kai 1095.
Fiye da rabi na adadin, an same su ne cikin jihar Legas a cewar alkaluman ta Cibiyar NCDC.
Daga cikin masu cutar a Nijeriya, mutum 32 suka mutu a yayin da 208 suka warke.