Manjo Hamza Al-Mustapha, Shugaban Jami’an tsaron Tsohon Shugaban Ƙasar Najeriya Janar Sani Abacha, yayi zargin cewa Masu kuɗi dake da halin samo makamai, da manyan ƙwayoyi, sune matsalar tsaron dake fuskantar Najeriya.
Al-Mustapha ya bayyana cewar magance matsalar, yana buƙatar gudunmuwar kowa da kowa da suke da kishin Ƙasar, a yayinda su kuma Hukumomi dole su yi wani yunƙuri domin samar da tsaro a Ƙasar.
Manjo Al-Mustapha ya bayyana haka a wata zantawa da sashen Hausa na VOA inda yace “wannan lokaci ne da duk mai kishin Najeriya, wanda duk keda Najeriya da Africa a ransa, da ma duniya baki ɗaya, daya tashi tsaye domin bada gudunmawa akan matsalolin dake faruwa. Al’amari na tafiya kamar yadda yake.”
KARANTA WANNAN LABARIN: Adadin Wadanda Aka Harbe A Jihar Colorado Sun Karu Zuwa Biyar Cewar ‘Yan Sanda
“Akwai mutanen dake ɓarnatar da kuɗin su domin su haddasa rikici, kuma suna samun nasara.”
Yace abubuwa marassa kyau na faruwa a ƙasar nan, a yayinda wasu ƴan kaɗan suke da ƙarfin haƙar ma’adanan ƙasa.
Ya kuma yi zargin cewa wasu ƴan kaɗan ne ke amfana da arziƙin ƙasar nan ba tare da tunanin tsayawa ba, kuma idan kace zaka tsaida su, to zasu yi amfani da dukkanin ƙarfin su domin yaƙar mutum, kuma zasu yi hakan da masu taimaka masu na cikin gida da waje.
Comments 1