Motocin, ababan hawa da sauran harkokin tattalin arziki sun tsaya cik na tsawon sa’o’i da dama a jiya, yayin da masu zanga-zangar galibin manyan motoci suka tare hanyar Gwaram zuwa Basirka a jihar Jigawa.
Kungiyar tasu ita ce ta ci gaba da rufe babbar gadar Gwaram wacce ta hade jihar Jigawa da Bauchi da Gombe.
Idan dai za a iya tunawa, a watan Agusta ne gwamnatin jihar ta sanar da rufe gadar ga manyan motoci a wani mataki na gudanar da gyare-gyare a sassan gadar da ta lalace.
Masu zanga-zangar wadanda galibinsu matasa ne, sun tare hanya inda suka hana ababen hawa zuwa daga bangarorin biyu.
Yayin Matafiya da za su je jihohin Bauchi da Gombe daga jihohin Kano da Jigawa sun shafe sa’o’i da dama a kan hanya.
An tilasta wa matafiya sauka da tafiya zuwa wancan gefen hanya don ci gaba da tafiye-tafiye.
Sai dai jami’in ‘yan sanda reshen Gwaram, SP Mohammed Wakili da masu ruwa da tsaki da kuma Hakimin Gwaram sun kwantar da hankulan masu zanga-zangar da suka amince da bude hanyar bayan da suka baiwa gwamnati wa’adin kwanaki uku da ta samar da wata hanyar da za su bi da motocinsu.