Rundunar Yansanda ta Jahar Katsina ta samu nasarar cafke wasu mata su 3, da suke safarar man fetur zuwa Magamar Jibia domin siyarwa ga yan ta’addan daji.
Masu safarar man dai suna amfani ne da wata dabara ta sanya man a cikin jikkuna Kamar matafiya.
Mai magana da yawun Rundunar Ƴan Sandan Jahar SP Gambo Isah, ya gabatar da masu laifin ga Manema labaru, a yayin wani taro a madadin kwamishinan yan sandan Jahar CP Sanusi Buba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mun amince a tura tubabbun ƴan Boko Haram cikin jama’a — Cewar Shehun Borno
Kamar yadda Kakakin Rundunar SP Gambo Isah ya bayyana, waɗanda aka cafke ɗin, dukkaninsu, sun kasance mazaunan Unguwar Malali a cikin Birnin Katsina.
Waɗanda aka cafke ɗin, sun bayyana cewar suna sayar da man fetur ɗin ne ga masu Mashina idan sun isa a Magamar Jibia, inda su kuma za’a ƙirga kuɗinsu a biyasu.
Sun Kuma maganta akan dabarar da suke bi wurin sayen man, a gidajen mai wanda suke a nan cikin Birnin Katsina.
Idan dai za’a iya tunawa, Rundunar Yan Sandan a ƴan kwana kin nan, tana cigaba da samun nasara, ta fuskar cafke masu safarar man fetur da sauran kayan masarufi ga ƴan ta’adda dake cikin dazuka.
A wani Labarin kuma
Mutum daya ya mutu yayin da wasu uku suka samu raunuka bayan wani gini ya rufta a yankin Woji na garin Fatakwal a jihar Rivers.
Wakilin majiyar Jaridar Dimokuradiyya ya gano cewa, lamarin ya faru ne da yammacin jiya Laraba.
Daya daga cikin wadanda abin ya rutsa da su, ya dora alhakin hakan a kan ruwan sama kaman da bakin kwarya da akasami a yankin aranar Talatar data gabata, wanda ya ce, ya shafi gine-gine da dama wadanda ba’a kammala ba.
Wanda abin ya rutsa da shi ya ce, mutum daya ya rasa ransa sanadiyar lamarin, yayin da wasu mutane uku suka samu mummunan raunuka daban -daban.
“Ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi a ranar Talata wanda ya shafi tubalin ginin, shi ne ya sa ginin ya rushe” inji shi.
“Ruwan ya yi tsanani sosai, kuma tuni ambaliyar ruwar ta sanya asarar dukiyoyi sosai a yankin” a cewar shi.
Kazalika ya ce, “Mutum daya ya mutu a lamarin, yayin da wasu mutane uku da suka samu raunuka, kuma an kwashe su zuwa asibiti domin duba lafiyar su,” in ji shi.
Wakilin jaridar Daily Trust yayi duk Mai yiwuwa wajan hi ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar Rivers, SP Nnamdi Omoni game da lamarin, har zuwa lokacin hada rahoton Amma abun ya citira.