Ifeanyi Ejioefor lauya mai kare Jagoran masu fafutukar kafa kasar Biafra Nnamdi Kanu yace ana gaf da sakin shi.
Ejioefor ya bada tabbacin babu wani kwakwkwaran dalili da zaisa a cigaba da tsare Nnamdi Kanu. Kamar yadda Jaridar Pmnews ta wallafa
Yayi kira ga yan Biafra da su kara hakuri kuma su cigaba da addu’a.
KARANTA:- Abunda ya zama dole Buhari yayi akan BIAFRA da ODUDUWA: Mogholu
“Ina da kwarin guiwar da nan da dan lokaci kadan zai fito daga magarkama, iyaka dai tuhumarsa sukeyi, babu wani babban dililin da zai sa su cigaba da tsare shi.”
Ejioefor yace “Nnamdi Kanu na cikin koshin lafiya, duk da cutar dashi da akayi a kasar Kenya.”
Kamar yadda yace ” kada ku sami damuwa babu abunda ke damun shi yana cikin koshin lafiya, sai dai an hanashi ganawa da iyalansa, musamman ma matar sa da yaran sa, wanda hakama wata hanya ce ta azabtar da mutum.
“Muna iya bakin kokarin mu don a sauya masa wajan zama, sannan mu samo kwararren likitan da zai cigaba da kulawa dashi.”
Da aka tamabayeshi kan masu farautar sa shi lauyan.
Yace “Babu wani barazana ko azabtarwa da zai sanya na dena Kare Nnamdi Kanu, Ina baiwa wadanda ke farauta ta shawara da su kara tunani don ba wanda zai iya kashe ni.”
” Ni zabin Allah ne, ya zabe ni na zama lauyan Nnamdi Kanu da kuma Biafra, zan cigaba da tsaya masa har sai gaskiya tayi halinta, kawai abunda mukeso da Yan Biafra su cigaba da addu’a kuma su kara hakuri.”
“Ku cigaba da masa addu’a da kuma mu lauyoyinsa.”
Da ake tambayar sa kan zaman da za’ayi a Kotu a ranar 26 ga watan July cewa yayi “Babu wani abu na daban da zai faru, zamuje mu gabatar da hujjojinmu”