Masu Ruwa da Tsaki sun shawarci Kwalejojin Kimiyya akan bincike, haɗa hannu da Ma’aikatu
Masu Ruwa da Tsaki a ɓangaren Ilmi a ranar Litinin sun yi kira ga Kwalejin Kimiyya ta Ado Ekiti, data haɗa hannu da Ma’aikatu a matsayin wani ɓangare na inganta tattalin arziki da kuma makomar makarantar.
Masu ruwa da tsakin,
Sun yi jawabi a taron farko na wuni biyu akan Tattalin Arziki.
KARANTA WANNAN LABARIN: DA DUMI-DUMI: Kotu ta yankewa tsohuwar minista, tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP, hukuncin zama gidan yari
Shugaban Makarantar Sufiyo ta Kasa dake Oyo, Dr Dupe Olayinka-Dosunmu Wanda ya yi kira ga Kwalejin Kimiyya data yi kyakkyawan amfani da Albarkatun dake gare ta na Ƙwararru wajen yin ayyuka ga Al’umma, ya kuma yi kira a garesu dasu tashi tsaye wajen bincike, wanda zai samar da sakamako mai kyau.
A cewar sa ta la’akari da irin mahimmancin Kwalejojin Kimiyya a tattalin arzikin Najeriya, do ta tashi wajen yin ƙirƙire-ƙirƙire.