By Abbas Yakubu Yaura
Mambobin kungiyar masu gidajen burodi na kasa, da masu sayar da burodi na Najeriya, reshen jihar Imo a ranar Litinin din nan sun ce sun kammala shiri tsaf na rufe harkar samar da burodi a jihar.
Shugaban kungiyar na jihar Osmond Nkeoma ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Owerri.
Ya bayyana cewa dalilin daya sa zasu rufe wuraren samar da burodin shine ci gaba da samun tashin gwauron zabi na kayayyakin da ake samarwa a kasuwanni.
Nkaoma ya ce: “Kudin dizal, mai, sukari ya wuce gona da iri da masu yin burodin za su iya samu. Mun damu musamman game da farashin dizal, man kayan hadi da sukari, babu abin da za mu iya yi ba tare da waɗannan samfuran ba.
“Farashin Diesel ya karu, yanzu ana sayar da litar sa akan Naira 600 zuwa sama, sukari iya na kamfanin Dangote ne kadai ya ke samuwa, sannan ba ma ganin wasu kamfanoni kamar Bua.
Kazalika yace yanzu buhun sikari da muke saye a kan Naira 20,500 ada, yanzu ana sayar da shi kan Naira 25,000, mai da muke sayan sa a kan Naira 26,000 yanzu ana sayar da shi kan Naira 35,000.”
Ya kuma roki gwamnatocin jihohi a dukkan matakai da su duba irin kalubalen da masu yin burodi ke fuskanta a kasar nan.