By Abbas Yakubu Yaura
Shuaibu Wa’alamu, mahaifin wata yarinya ‘yar shekara takwas mai suna Asma’u, wanda ake zargin makwabcinsa ne ya kashe ta a Zariya da ke Jihar Kaduna, ya koka da yadda wasu suka sace tare da kashe ‘yarsa duk da karbar kudin naira miliyan 3m a matsayin kudin fansa.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da wani malami ya sace tare da tsare wata yarinya ‘yar shekaru biyar da haihuwa, mai suna Hanifa Abubakar bayan ya karbi kudin fansa naira miliyan 6m a Kano.
Asmau, wacce aka ce ta shafe kwanaki 42 a hannun wadanda suka sace ta, an ce daya daga cikin makwabtan su ya tsare ta a ranar 9 ga watan Disambar shekarar data gabata 2021, kamar yadda mahaifinta ya bayyana.
An sami (Asmau) ne a hannun wadanda suka sace ta bayan sun karbi naira miliyan 3m daga hannun iyayen.
Tunda farko labarin wanda wani abokin mahaifinsa mai suna Musa Ahmed ya fara yadawa a shafin Hausa Fulanin a Instagram, ya nuna cewa an yi garkuwa da karamar yarinyar ne a lokacin da take kan hanyarta ta sayen katin waya.
Sanarwar ta kara da cewa, “An sace tare da tsare ‘yar abokina, ‘yar shekara takwas a kan hanyarta ta sayen katin waya a unguwarmu.
“Kwanaki 42 da suka gabata tana tare da wadanda suka sace ta wadanda suka bukaci a ba su kudi naira miliyan 3m, amma abin bakin ciki sai suka kashe yarinyar daga karshe.”
“Sun kira mahaifinta suna neman a kara masu kudi wanda ya wajabta kuma ya tura wani da kudin.“A yayin da ake jiransu, mutumin ya fusata sosai saboda yanayin sanyi da dare. Ya kira mahaifin ya sanar da shi bai ga kowa ba tukuna.
“Sai mahaifin ya kira lambar ya ce su fada masa gaskiya idan sun kashe yarinyar. Ga shi, sun ce, sun kashe ta, sun binne ta a cikin kabari marar zurfi, kwanaki huɗu da suka wuce.”
Da yake magana da manema labarai a Zariya a ranar Asabar, Wa’alamu ya ce an sace ‘ya ta ne a ranar 9 ga watan Disamba shekarar 2021, kuma nan take na kai karar zuwa ga ofishin ‘yan sanda bayan ya kasa mayar da diyarta ta koma gida.
Ya ce bayan ‘yan kwanaki masu garkuwa da mutanen sun tuntubi ‘yan uwa inda suka bukaci a biya su kudin fansa naira miliyan 15m da aka tattauna dasu aka cimma matsaya aka ba wadanda suka sace naira miliyan 2m.
A cewarsa, daga baya ‘yan barayin yarinyar sun yi waya tare da neman karin Nnaira miliyan 1.045m a matsayin sharadin sakin yarinyar.
Sai dai har yanzu rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ba ta tabbatar da faruwar lamarin ba domin babu wani martani daga mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, Mohammed Jalige, lokacin da aka tuntube shi har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
Comments 1