Masu sharhi na ganin babbar abokiyar hamayyar Barcelona, wato Real Madrid ka iya zama kalubale ga aniyarta ta lashe kofin gasar Copa del Rey karo na 5 a jere, la’akari da farfadowar karsashin kungiyar ta Real Madrid a karkashin jagorancin Santiago Solari.