Masu yin burodi karkashin inuwar kungiyar masu sana’ar burodi ta kasa (PBAN), sun koka da yadda ake fuskantar wahalar gudanar da buredi a Najeriya sakamakon tsadar kayayyaki.
Wata sanarwa da shugaban kungiyar PBAN, Emmanuel Onuorah, da jami’in hulda da jama’a da masana’antu, Babalola Thomas suka fitar tare da sanya hannun hadin gwiwa a ranar Talata, ta ce sun kammala shirin janye ayyukansu da shiga yajin aikin daga ranar Alhamis 21 ga watan Yulin 2022 na tsawon kwanaki hudu, a matsayin misali na farko.
“Biredi babban abinci ne kuma daya daga cikin mafi arhar abinci da ake samarwa ga talakawa da masu arziki. Don haka ya zama wajibi gwamnatin tarayya ta lura da hakan tare da tabbatar da dorewar masana’antar,” in ji sanarwar.
Ya kara da cewa, “A wani mataki na tabbatar da wanzuwar masana’antun yin burodi a Najeriya, mun yanke shawarar janye ayyuka tun daga ranar Alhamis 21 ga watan Yuli, 2022 na tsawon kwanaki hudu a matakin farko, kuma inda ba a shiga tsakani ba daga gwamnati, za mu kara tsawaita lokacin yajin aiki.”
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Sanarwar ta kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta daina cajin kashi 15 na harajin noman alkama kan shigo da alkama.
Haka kuma ta bukaci hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) da ta yi nazari a kasa kan hukuncin Naira 154,000 da ake tuhumar gidajen borodi kan sabunta izini.
Kungiyar ta bayyana cewa farashin kayayyakin burodi ya tashi inda ta nemi tallafin da rancen lamuni da babban bankin Najeriya CBN ke baiwa kananan masana’antu, da matsakaitan masana’antu (MSMEs).
Ta kuma nemi a dakatar da abin da ta kira ka’idojin kamfanoni masu yawa na masana’antar yin burodi.
PBAN, ta bayyana cewa kungiyar ‘yar uwarta ta dade tana ganawa da ma’aikatar masana’antu, kasuwanci da zuba jari ta tarayya a Abuja (FMITI) tun daga shekarar 2021, ta bayyana cewa babu wani abu da ya fito daga wannan kokarin na cigaba.
A watan da ya gabata, kungiyar manyan masu yin burodi da masu abinci (AMBCN) ta yi barazanar cewa mambobinta za su janye ayyukansu a fadin kasar saboda wannan lamari.
A cikin wata sanarwa da AMCN ta fitar, ta bayyana cewa, farashin fulawa da sikari da sauran kayayyakin da ake amfani da su wajen sana’ar biredi sun yi tashin gwauron zabi ta yadda masu yin biredi da yawa ba za su iya samu ba.