Wutar Man Fetur ta tashu a Sansanin Jami’an wanzar da zaman lafiya na majalisar dinkin duniya dake Beni a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, a daidai lokacin da ake zanga-zangar adawa da zaman jami’an a kasar
Akalla wasu sansanonin Jami’an wanzar da zaman lafiyan guda biyu ne aka kai wa hari a jya Alhamis. Sai dai ba a bayyana adadin wadanda suka jikkata ba.
Akalla mutane 19 da suka hada da jami’an wanzar da zaman lafiyan uku ne suka rasa rakuyansu a rikicin, da ya biyo bayan zanga-zangar kin jinin Jami’an na Majalisar Dinkin Duniya da aka faratun ranar Litinin din da ta gabata.
BBC Ta ruwaito cewa masu zanga-zangar na zargin Majalisar Dinkin Duniya da rashin kare fararen hula daga kungiyoyin masu dauke da makamai da ke kai hare-hare a gabashin kasar.
KARANTA WANANN LABARI: Gwamnatin Jihar Kebbi Ta Ayyana Litinin A Matsayin Ranar Hutun Sabuwar Shekarar Musulunci
Da yake jawabi Mai magana da yawun Majalisar Dinkin Duniya ya ce masu zanga-zangar sun hada kai da kungiyoyin mayaka da ake kira Mai Mai.
Haka kuma fiye da kungiyoyi 100 daban-daban masu dauke da makamai ne ke cigaba da kai farmaki a gabashin kasar ta Jamhoriyar Dimokiradiyyar Congo, ciki har da Allied Democratic Front da ke da alaka da kungiyar IS.
A halin da ake ciki kuma, hare-haren baya-bayan nan sun yi sanadiyar mutuwar daruruwan mutane tare da raba dubbai da muhallansu.
A wani labarin kuma na daban.
Tsohon Karamin Ministan Ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba, da wata kungiya mai suna Incorporated Trustees of Rights for All International, sun shigar da sammaci a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja suna neman ta ba da umarnin ayyana Nwajiuba a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC.
Sun kuma roki kotun da ta soke kuri’un da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, da kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya samu.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Nwajiuba wanda ya zargi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC da ba da cin hancin ga daliget da daloli ya gabatar da batutuwa 26 domin tantancewa a kotu.
Ya kuma bukaci kotun da ta tantance ko adadin ya ci karo da sashi na 11 (A) 12(1) da 13(1) na kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC.
Tsohon ministan ya bukaci kotun da ta tantance ko adadin wakilan da za a yi zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP bai sabawa sashe na 33(1) da (5) (c) na kundin tsarin mulkin jam’iyyar ba.
Ya roki kotun da ta tantance ko idan aka yi la’akari da bayyananniyar sharuddan da ke tattare da sashe na 6 (6) (A) (B) da (C) da aka karanta tare da sashe na 15 (5) na Kundin Tsarin Mulki na 1999, kotun ta na da ikon shari’a na sokewa, da kuma ayyana zabukan a matsayin haramtattun zabukan fidda gwani na shugaban kasa na APC da PDP.
Nwajiuba ya bukaci kotun da ta tabbatar da cewa duk kuri’un da aka kadawa Tinubu da Atiku a babban taron kasa musamman na jam’iyyun APC da PDP sun sabawa doka, ba su da wani tasiri, kuma ba su da wani amfani a kan dalilan cin hanci da rashawa da sayar da kuri’un daliget don su jefa musu kuri’a.
A karshe ya roki kotun da ta yanke hukuncin cewa, dangane da karin bayani na sakin layi na 1 da na 8 na kundin tsarin mulkin 1999 na 5, zargin cin hanci da rashawa da Tinubu da Atiku ke yi na sayen kuri’u da kuma jawo wakilai da daloli da Naira domin su samu kuri’u a babban taron kasa na musamman, ya hana su ci gaba da neman, tsayawa takara, da rike mukamin shugaban kasa.