Masu zanga-zanga a Sri Lanka sun cinna wa gidan Firaiminista Ranil Wickremesinghe wuta.
A ƴan sa’o’in da suka gabata ne dai masu zanga-zangar suka afka gidan shugaban ƙasar da ke Colombo.
Mamayar gidan shugaban kasan Sri Lanka a yau na zuwa ne bayan watanni da masu zanga-zanga suka dauka suna yi a fadin kasar saboda karewar kudaden waje da kasar ke fama da shi.
Wanda hakan ya sa samun kayayyakin amfanin yau da kullum kamar su fetur da magani da abinci suka yi karanci.
Hakan ne ya sanya gwamnatin Sri Lanka ta dakatar da sayar da man fetur ga mutanen kasar har zuwa ranar Lahadi, inda ake iya cewa ita ce kasa ta farko da ta yi hakan tun shekarun 1970.
A makon da ya gabata, hukumomin ƙasar sun bayyana cewa man fetur ɗin ƙasa da mako ɗaya ne kawai ya rage a kasar wanda motocin bas da jiragen kasa da kuma motocin daukar marasa lafiya za su yi amfani da shi.
An rufe makarantu a fadin kasar, inda aka umarci ‘yan kasar da suka kai miliyan 22 yin aiki daga gida.