Gwamnatin jihar Kadunata bayyana cewa ta karbi kashin farko na sojoji mata 100 daga cikin 300 da aka aika hanyar Kaduna zuwa Abuja domin wanzar da tsaro.
A ranar Laraba ne dai rundunar sojin kasar ta sanar da aike sojoji mata 300 zuwa hanyar domin shawo kan matsalar masu garkuwa da mutane a kan hanyar.
An kwaso sojoji matan ne daga runduna ta daya ta sojin kasar da ke jihar Kaduna, kuma kuma an hada su da rundunar sojojin kasar ta mata domin yin aiki tare.
Gwamna jihar Kaduna Nasir El-Rufa’i ya karbi tawagar matan, wadda ita ce rukunin farko da za su zauna a masaukinsu da ke Kakau a kan hanyar ta Abuja.