Mata Suna Buƙatar Samun Kuɗi Kafin Su Shiga Siyasa — Inji Mai Sharhi
Wata mai sharhi kan al’umma, Mariya Ibrahim ta buƙaci mata da su kasance masu ƴancin cin gashin kansu kafin su shiga harkokin siyasa.
Ibrahim ta bayyana hakan ne a lokacin da ta bayyana a gidan Talabijin na Trust TV a ranar Juma’a.
“Mata na buƙatar ƙarfafawa. Kafin in shiga siyasa sai da na samu kudina,” inji ta.
KARANTA WANNAN LABARIN: Tinubu Yafi Kowane Ɗan Takara Sauƙin Talla Saboda Irin Ƙudirorin sa – Keyamo
Mai sharhin al’umma ta jaddada cewa kamata ya yi mata su shiga siyasa da tunanin yin hidima ba wai don neman kuɗi ba kasancewar siyasa ba sana’ar neman kuɗi ba ce.
“Ba ka shiga siyasa don neman kuɗi, ka shiga siyasa don yin hidima. Don haka idan ba ku da kuɗi, za ku iya aiki? Ka je ofishin da kake tsammanin wani abu daga shugaban ko wani… ba daidai ba ne, to za a raina ka. Abu mafi mahimmanci ga mata shine a ba mu iko. Su zama ƴan kasuwa, su kafa wani abu su samu kuɗin shiga sannan sai su fara daga nan”
Ta bayyana cewa akwai buƙatar iyaye su ƙarfafa ƴaƴansu da kuma horar da su yadda ya kamata don shirya su don tunkarar haƙiƙanin rayuwa.
“Idan ka kalli Nijeriya ta yau ka kwatanta ta da namu na zamaninmu, iyaye suna gabatar da ‘ƴaúansu suna fallasa kuɗi yadda suka ga dama. Lokacin da muke girma, kudi ba ya nufin wani abu a gare mu, abin da ke da mahimmanci shine samun asali, amma a yau ba haka ba ne.
“Iyaye suna lalatar da ’ya’yansu da kuɗi… yara suna buƙatar horaswar tarbiyya. Dole ne ku ba yaranku tarbiyya mai kyau ta yadda idan sun girma suka koma cikin al’umma su samu kyakykyawan sakamako”.