Mataimakin Kwamishinan ‘yan sanda mai lura da aikin tantance masu son shiga aikin dan sanda a jihar Sakkwato ya rasu. Ya rasu ne da safiyar ranar Litinin a yayin da ya bar wurin kwanansa zai kama hanyar dawo wa birnin tarayya Abuja bayan ya kammala aikinsa a jihar.
Rahotanni sun bayyana cewa, Kakakin ‘yan sandan jihar Sakkwaton, DSP Muhammad Sadiq, ya tabbatar da mutuwar ACP Zubairu. Inda ya ce; “Ya kammala aikinsa ke nan a Sakkwato na tantance masu son shiga aikin dan sanda wanda aka kammala a ranar Asabar.” In ji shi. Inda ya kara da cewa; “Bai yi korafin rashin lafiya ba, yana cikin koshin lafiya. Mun kadu da samun labarin rasuwarsa.” Kamar yadda ya tabbatar.
Jaridar Daily Trust sun labarto cewa; tuni iyalan mamacin suka iso Sakkwato domin yi masa jana’iza.
Babban Limamin Masallacin Abu Huraira, Dr. Mansur Ibrahim ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa; za a yi masa sallar Jana’iza a masallaci a ranar Talata. Ya shawarci al’ummar Musulmi dake yankin da su zo wurin jana’izar da misalin karfe 9 na safe. Sannan ya yi masa addu’ar Allah yasa aljanna makoma.
Rahotanni sun nuna cewa mamacin dan jihar Adamawa ne, inda yake aiki a babbar hedikwatar ‘yan sandan dake Abuja, kafin a aike shi Sakkwato kan wannan aikin na musamman.