Mataimakin shugaban kasa yemi Osinbajo, da shugaban majalisar Dattawa Bukola Saraki, sun halarci taron da aka shiryawa sabbin Gwamnoni da Wanda zasu koma kujerar su a karo na biyu.
A karkashin kungiyar Gwamnoni wace gwamnan Zamfara Abdul’aziz yari, ke shugaban ta, Inda yayi kira garesu kan su maida hankali kan harkar noma Wanda shine zai kara kawo wadatar tattalin arzikin kasa.
Taron Wanda aka fara tun 28 ga watan Afrilu zai ci gaba har 1 ga watan mayu mai zuwa.
A gefe Guda taron Ya samu halartar sakataren Gwamnatin tarayya Boss Mustafa, da kuma jigo a jam’iyyar APC Bola Tinubu.