Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, SAN, zai wakilci Najeriya a wasu taruka a gobe da kuma ranar litinin, a yayin jana’izar marigayiya Sarauniya Elizabeth ll a kasar Ingila.
Osinbajo zai bar Abuja ne a ranar Asabar din nan don halartar taron dangin sarauta, da shugabannin kasashen duniya – ciki har da mambobin kungiyar kasashe rainon Ingila, shugabannin kasashe duniya, manyan gwamnoni, firaministoci, da kuma iyalan sarakunan kasashen waje – a wajen bukukuwan, ciki har da bikin jana’izar da aka shirya gudanarwa a Westminster Abbey ranar Litinin.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Gabanin jana’izar, mataimakin shugaban kasar zai kasance cikin manyan baki da Sarki Charles lll da Sarauniya Consort Camilla za su tarbe su, a wata liyafar za a yi a fadar Buckingham, ranar Lahadi, a cewar wata sanarwa da Laolu Akande, kakakin mataimakin shugaban kasar ya fitar.
Karanta kuma: Osinbajo Ya Ketara Zuwa Kenya Domin Wakilatar Buhari
“A farkon wannan rana, mataimakin shugaban kasar zai gudanar da taron kasashe biyu tare da sakataren harkokin wajen Birtaniya, James Cleverly.
“Sarauniya Elizabeth ll ita ce Shugabar kasashe rainon Ingila kuma wacce ta fi dadewa a kan sarautar Burtaniya. Ta rasu tana da shekaru 96 a ranar 8 ga watan Satumba na wannan shekara a gidan Balmoral na Scotland.
“Mataimakin shugaban kasar zai dawo Najeriya bayan jana’izar ranar Litinin,” in ji sanarwar.
A wani labarin kuma: Najeriya Tana Mataki Na Karshe Na Rugujewa — Dan Takarar Shugaban Kasa
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a zaben 2023, Peter Obi, ya ce Najeriya na cikin mataki na karshe na rugujewa kuma dole ne a gaggauta ceto kasar.
“Najeriya a yanzu ba a cikin shirin rugujewa kadai ta ke ba, a mataki na karshe ta ke na rugujewa. Mutanen Arewa ba su da wurin tsaro, ba su da hanyoyi masu kyau, ba sa sayen biredi da rahusa fiye da mutanen kudu. To, su ne mutanen kudu,” in ji tsohon gwamnan jihar Anambra a ranar Juma’ar nan a CNN yake bayyana haka.