Wasu manyan lauyoyi biyu, sun ce bijirewa umarnin kotun koli da babban bankin Najeriya ya yi ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar.
Manyan Lauyoyin na mayar da martani ne kan kin bin umarnin Kotun Koli da CBN ya yi a makon jiya da ta hana shi aiwatar da wa’adin ranar 10 ga Fabrairu kan Tsofaffin kudi. DAILY POST ta rawaito.
KU KARANTA: Majalisar Dinkin Duniya Ta Nemi Agajin Makudan Kudi Don Tallafawa Ukraine
Mista Harris Gbole, Babban Lauyan Najeriya; da Kehinde Eleje, lauya; sun bayyana hakan ne a lokacin da suke karin haske kan halin da ake ciki, dangane da tsohon kudin, yayin wata hira da gidan talabijin na Channels a ranar Laraba.
A nasa bangaren, Gbole ya bayyana cewa, abin da CBN ke yi ya saba wa Kotu kuma ya saba wa doka.
Ya ce hakkin kowa da kowa ne su bi umarnin kotu, yana mai bayyana matakin na CBN a matsayin abin takaici.
“Sai dai jiya ko makamancin haka, sun sake dagewa cewa wa’adin ranar 10 ga Fabrairu ya tsaya, wanda hakan cin mutunci ne ga kotun koli da shari’a, abin takaici ne.”
Eleje ya bayyana cewa kasar na cikin rudani sakamakon bijirewa umarnin kotu na CBN.
“Muna fuskantar rashin zaman lafiya ne saboda yawancin ‘yan Najeriya ba sa yin mu’amala da na’urar lantarki, musamman wadanda ke yankunan karkara.
A ranar Talata, yayin da yake jawabi a Abuja, Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya bayyana cewa babu bukatar kara wa’adin ranar 10 ga watan Fabrairu.
A wani labarin kuma: Kotun Koli Ta Ɗage Shari’ar Daina Karbar Tsofaffin Kuɗi A Najeriya
Kotun kolin Najeriya ta dage ci gaba da shari’ar kan shirin sauya fasalin naira da babban bankin Najeriya CBN yayi.
DIMOKURAƊIYYA ta rawaito cewa yanzu haka kotun Kolin ta dage sauraren shari’ar zuwa ranar Laraba 22 ga watan Fabrairu domin sauraron kararrakin da jihohi 10 suka shigar.