Shugaban kamfanin jiragen Air peace, Mista Allen Onyema, ya yaba wa matakin da gwamnatin Najeriya ta ɗauka na hana shigowar jiragen sama daga wasu ƙasashe.
Matakin ya biyo bayan yunƙurin gwamnati na buɗe hada-hadar jiragen sama zuwa ƙasashen waje.
Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika, ya bayyana a ranar Alhamis cewar, jiragen ƙasashen da suka yarda ‘yan Najeriya su shiga ƙasarsu ne kaɗai za a ba damar shigowa Najeriya.
Sirika ya kuma ce an ɗauki matakin ne domin a kare martabar ‘yan Najeriya a ƙasashen da aka hana su shiga.
Onyema ya ce hakan zai ƙara daga darajar ‘yan Najeriya a idon duniya da kuma nuna wa jiragen ƙasashen wajen cewar Najeriya ba za ta ƙara ɗaukar raini ba.
A wasikar da Onyema ya aika wa Ministan ya ce, matakin ya kawo sabon sauyin ci gaba da hukumar sufurin jiragen ta samu.
“Lallai matakin da ka ɗauka zai kawo wa ‘yan ƙasar nan mutunci. ‘Yan Najeriya a faɗin duniya za su riƙa tafiya a mutunce tun daga ranar da wannan labarin ya kai musu.
“Wannan wani sabon babi ne na kawo ƙarshen tsangwama da ake yi wa ‘yan Najeriya da duk wani abu da ya fito daga ƙasar nan”, inji Onyema.
Ya kuma yaba wa Sirika kan sauye-sauyen da ya kawo a harkar sufurin jiragen sama, da kuma ƙoƙarin ganin jiragen Najeriya kawai suka yi jigilar ‘yan Najeriya da gwamnatin tarayya ta kwaso daga ƙasashen waje.