Akwai yiwuwar tattalin arzikin duniya ya farfado a shekara mai zuwa, sai dai ana hasashen duk da farfadowar tattalin arzikin, adadin wadanda suke fama da Talauci a duniya ba za su sauya ba a wannan shekarar sakamakon annobar cutar Korona da ya mamaye duniya, kamar yadda bankin dunniya ya fitar a wani rahotonta a ranar Talata.
Bankin duniya ya lissafa kasashe uku a duniya da suke da yawan masu fama da matsanancin talauci a duniya. Inda Bankin ya ce; kasashe kuwa sun hada da Indiya, wanda suke da kaso 24, sai Nijeriya da take da kaso 12, sai kasar Jamhuriyyar Dimokuradiyyar Congo da kashi 7, kuma Bankin ya ce duba da yadda kasashen ke tafiya tare da hauhawar al’umma, matsanancin Talaucin zai ci gaba da zama a wadannan kasashen.
Wannan hasashen na zuwa ne bayan da wata ma’aikata dake birnin Washington na kasar Amurka a ranar Litinin ya fitar da cewa annobar cutar Korona ka iya jefa mutum miliyan 70 zuwa 100 cikin matsanancin Talauci a cikin 2020 a daidai lokacin da tattalin arzikin duniya ya fada halin tasku da ba a taba ganinsa ba cikin shekaru 80.
Kafin annobar cutar Korona, ana bayyana wanda yake cikin matsanancin Talauci da wanda yake rayuwa kasa da Dala 1.90 a kowacce rana. Inda kuma yanayin ke karasa kasa a yanzu.
Bankin ya ce akwai yiwuwar a samu ci gaba da kashi hudu a cikin shekarar 2021.
Bankin har wala yau ya gargadi yankin Kudancin Asiya da cewa suma za su iya fuskantar karin matalauta sakamakon Annobar cutar Korona din musamman ma a kasar Indiya.
Cikin mutum miliyan 176 dake fama da talauci, akwai yiwuwar a samu ci gaba su rika rayuwa a kasa da Dala 3.20 a kowacce rana, inda kashi biyu bisa uku suna rayuwa ne a Kudancin Asiya.