Biyo bayan taron sulhu da Ƙungiyar Masu Ɗaukar Hoto mai Motsi ta Najeriya haɗin gwuiwa da Ƙungiyar Masu Fina-finai ta Ƴan Kannywood (AFMAN) suka shirya, domin shawo kan matsalar cece-kuce dake yawo akan hirar da sashen Hausa na BBC yayi da fitacciyar jarumar Fim Ladin Cima, Ƙungiyar Masu Shirya Fina-finai ta Matan Kannywood (K-WAN) ta sanar da janye ƙarar data shigar akan Mawaƙin nan Naziru Ahmad Sarkin Waƙa.
A jiyane, Ƙungiyar Masu Shirya Fina-finai ta Matan Kannywood ta Najeriya K-WAN ta baiwa Mawaƙi Naziru Ahmad Sarkin Waƙa kwana uku domin ya baiwa matan Kannywood haƙuri ko ya fuskanci hukuncin doka akan abinda ƙungiyar ta bayyana a matsayin ɓata suna akan matan Kannywood dake cewa mata suna bada kansu domin a kwanta dasu domin a sanya su cikin shirin ɗaukan fim.
A cewar Ƙungiyar, an ɓata sunan matan dake cikin Masana’antar wanda mawaƙin yayi a dalilin maganganun sa, inda ya bayyana cewar wasu matan ana kwantawa dasu kafin a sanya su a shirin fim.
KARANTA WANNAN LABARIN: Shugaba Buhari Ya Janye Ganawar Sa Da Gwamnonin APC
Amma takardar janye ƙarar na cikin wata sanarwa da Jami’in hulɗa da Jama’a na MOPPAN Al-amin Chiroma ya fitar, bayan an gudanar da wani taron gaggawa na sulhu a Kano.
A cewar sanarwar, dukkanin waɗanda lamarin ya faru dasu da masu ruwa da tsaki na Masana’antar Kannywood sun halarci taron, inda suka ce lamarin dake faruwa a yanzu an shawo kan shi.
Ta kuma ƙara dacewa, sakamakon daya fito a taron ya hana duk wani rubutu a Kafafen Sadarwa na Zamani daya shafi lamarin Ladin Cima.
Sanarwar ta kuma bayyana akwai taron horaswa domin wayar da kan mambobin Masana’antar Kannywood akan yadda zasu yi amfani da Kafafen Sadarwa na Zamani domin hana faruwar irin waɗannan maganganu anan gaba.
Waɗanda suka halarci taron sun ƙunshi Auwalu Ismail Mashal, da Mustapha Naburaska (Mai baiwa Gwamnan Kano Shawara akan Kannywood) da Mohammad Ibrahim Gumel, da Hadiza Muhammad, da Abubakar Bashir Maishadda, da Musbahu M.Ahmad, da Naziru M. Ahmad, da Alhaji Ibrahim Mandawari da sauran su.