By Ishaq Dabai
Majalisar Zaman Lafiya ta Mata a Karamar Hukumar Dala ta Jihar Kano ta bi sahun kiraye kirayen da za a hukunta masu aikata laifukan da ke da nasaba da jinsi domin su zama masu hana wasu dake da niyyar aikata irin wannan laifi.
Jami’ar ci gaban mata ta Majalisar, Fatima Muhammad itace tayi wannan kiran yayin wani taron zauren gari wanda Majalisar Zaman Lafiya ta Mata ta shirya karkashin kungiyar ta (CIPP) don inganta Zaman Lafiya da wayar da kan mata a yankin da dokar hana cin zarafin mutane ta shekarar 2015.
Fatima ta nuna damuwarta kan yadda ake ci gaba da cin zarafin mata da kananan yara wanda ta danganta rashin karancin hukunci.A cewarta, “Shirin ya kasance don wayar da kan mata da yara mata kan yaddacza a kawo rahoton cin zarafin mata.
“Yakamata a sami hukunci mai tsauri akan masu karya doka saboda lokacin da yafi ƙarfin hakan zai zama abin hana wasu. Inda aka kyale masu keta doka su tafi kyauta ba tare da sanya sun fuskantar fushin doka ba, shine ke da alhakin ci gaba da cin zarafin kuma a wasu lokuta, iyaye suna yanke shawarar ba da rahoton karar ga hukumomin da abin ya shafa.
Ya kamata a hukunta irin bata garin maza masu yiwa mata fyade yayin da matan da ake cin zarafin yara maza da manyan maza yakamata a daure su daurin rai da rai. Domin irin wannan hukunci mai tsauri zai kawar da duk wata barazana a cikin al’umma kuma zai zama mai hana masu cutar da irin wannan mugun aiki a zukatansu, “in ji ta.
Jami’in Shirin na ARDA akan shirin CIPP a Kano, Faruk Umar Abdulsalam ya goyi bayan kiran da matan suka yi inda ya bayyana cewa hukunta masu cin zarafin bai isa ya tsoratar da mutane daga irin wannan munanan ayyukan ba da sanin cewa za a sake su ga al’ummarsu bayan zaman kurkuku.
A jawabinta, memba ta FIDA, Barista Fatima Ahmad tace dokar hukunce hukuncen da ake amfani da ita a Arewacin kasar nan ba ta kunshi wasu daga cikin wadannan laifuka da aka samu ba don babu dalilin hukunta irin wadannan masu laifi ba saboda haka akwai bukatar Gwamnatin Jiha ta dauki VAPP data shafi duk wadannan. aikata laifuka kuma ya faɗi irin hukuncin daya kamata a ba wanda aka samu da laifi.