Matar data ɗauko ƴan Ta’adda suka sace Fasto, ta buƙaci Kuɗin Fansa
An kama wasu mutane da ake zargi daga Jami’an Rundunar Ƴan Sandan Jahar Ogun kan zargin sace wani Fasto Mapai Samuel na Cocin Zoe Family, Odo-Eran, Abeokuta..
KARANTA WANNAN LABARIN: Malamin da aka kora kan cin zarafin Ɗaliba ya dawo Gidan Yarin Kuje, ya samu Beli
Matar da ake zargin tana garkuwa da mutane Ibikunle Opeyemi da Abokin ta Kadiri Jamiu, an kama su a ranar Alhamis biyo bayan samun kiran Gaggawar da ƴan sanda ofishin su na Aregbe.
Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan DSP Abimbola Oyeyemi a cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Alhamis, yace sauran wadanda ake zargin sun yi shiga ne irin ta Sojoji inda suka tsere.
Yace waɗanda ake zargin sun aikata lamarin a ranar Laraba da misalin ƙarfe 8 na dare, amma an kama biyu daga cikin su a safiyar ranar Alhamis.
Oyeyemi ya ƙara dacewa an gaya ƴan sanda cewa wasu mutane biyu sun yi shiga ta sojoji tare da wata mata, sun shiga coci a lokacin da Fasto ke Wa’azi da misalin ƙarfe 8, sun fita dashi da tsiya, sun kaishi inda ba’a sani ba.
“Ya ce ba’a daɗe da ɗaukar shi ba, suka kira suna buƙatar kuɗin fansa.
“Bayan jin wannan ƙwararrun ƴan sanda sun bi bayan su, inda suka gano wurin da suke tare da kamo su.