Babban dan Shaikh Zakzaky, Mohammed Ibraheem ya tabbatar da cewa gwajin da aka yi wa mahaifiyarsa na cutar korona ya tabbatar da tana dauke da cutar. Mahaifiyar ta shi wacce gwamnati ke ci gaba da tsare ta a kurkukun Kaduna tare da mijinta, Shaikh Zakzaky.
Mohammed Ibraheem Zakzaky ya tabbatar da hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a yau Alhamis 21 ga Janairun 2021. Inda ya ce sakamakon gwajin ya nuna cewa tana dauke da cutar.
Ya ce mahaifiyar ta sa ta ji wadansu alamomi ne a jikinta, inda hakan ya tilasta a gwadata kwanaki shida da suka gabata.
Cikakken bayani na tafe daga baya.