By Abbas Yakubu Yaura
Wata matar aure mai shekaru 25, Aminat AbduLateef, wadda ta samu ‘ya’ya uku a kwanan nan a asibitin jihar Osun da ke Ede, a ranar Lahadin da ta gabata ta yi kira ga ‘yan Najeriya masu kishi da su taimaka mata.
Aminat AbduLateef, a zantawarsa da manema labarai , ta ce ta haifi jariran ne ta hanyar yi mata tiyata.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa baya ga kayan aikin likita da aka siya, daga cikin kudin aikin Naira 55,000 da asibitin ya bukata, an biya naira 45,000 ne ta hanyar neman taimakon dangantaka.
Sannan ta kara da cewa mijinta, dan kungiyar ’yan banga, Qowiyu Akinloye, wanda zai iya taimaka mata, yana tsare a gidan yari na Ilesa bayan an kama shi a ranar 13 ga Mayun shekarar 2021 yayin fadan jama’a a Ede.
Ta kara da cewa, “Mijina dan kungiyar ’yan banga ne. Ba shi da laifi, amma an kira shi dan a sasanta rigimar da aka yi a Ede a lokacin faɗan jama’a, ya tafi can.Ya kasance yana tsare a Ilesa tun ranar 13 ga Mayun bara 2021.
“Na haifi jaririn ta hanyar tiyatar caesarean. Su ne na farko a wajena. Ina da ciki da kyar aka kama mijina. Iyalina da ’yan uwana suna taimaka mini, amma ina bukatar taimako daga ‘yan Najeriya masu kishin kasa don biyan kudin asibiti da kula da jariran.”
Ita ma da take zantawa da wakilinmu, kanwar mahaifin ‘ya’yan uku Jelifat Akinloye, ta ce baya ga kudin asibiti, an sanya jariran a kan abinci na musamman da iyalin ba za su iya ba.
Kazalika ta ce, “Jariran kanana ne kuma an ba su shawarar abinci na musamman. Tin na abincin zai kai naira 3,000.
“A gaskiya muna bukatar taimako daga gwamnati da masu kishin kasa don kula da jariran da kuma fitar da dan uwana daga tsare. Ba shi da wani laifi daga tuhumar da ake masa.”