Matar gwamnan jihar Anambra Mrs Ebelechukwu Obiano ta gina gida 28 ga zawarawan da suke zaune a yankunan karkara a jihar.
Matar gwamnan ta gina gidajen ne a karkashin gidauniyarta wanda ba mallakin gwamnati ba mai suna ‘The Caring Family Enhancement Initiative (CAFE).
Ebelechukwu ta bayyana hakan ne a kauyen Umuru village dake karamar hukumar Nnobi, Idemili South a jihar a yayin da take mika makullan gida mai dauke da dakunq uku ga daya daga cikin wanda suka amfana da ginin wato Mrs Regina Maduka a ranar Talata. Ta tabbatar da cewa ta yi wannan aikin ne domin saukaka wa wadanda ba su da shi a cikin al’umma.
Ta ce tana jindadi ta ga talakawa da zawarawa suna kasancewa cikin farin ciki. Saboda a cewarta yanzu suna da muhallinsu. Ta nuna gamsuwarta na yadda gidauniyarta ke tallafawa gajiyayyu.