Matar gwamnan jihar Kwara, Olufolake Abdulrazaq, a ranar Juma’a a garin Ilorin, ta raba kayan tallafi na abinci ga marasa galihu dake cikin al’umma.
Wannan tallafin ta yi shi ne a karkashin kungiyar matan gwamnonin Arewa, a wani mataki na tallafawa al’ummar da ba su da karfi musamman a daidai wannan lokaci na zaman gida da dokar hana fita.
Rahotanni daga majiyarmu sun tabbatar da cewa fiye da mutum 200 marasa galihu ne suka amfana daga wannan tallafin.
Da take mika kayayyakin tallafin, matar gwamna Abdulrazaq ta shawarci ‘yan Nijeriya da su rika taimakon Talakawa da kuma wadanda ba su da galihu domin rage musu radadin talauci.