Uwargidan gwamnan jihar Ogun, Misis Bamidele Abiodun, ta yi kira ga ‘yan Najeriya da kada su yi sakaci da masu shaye-shayen miyagun kwayoyi a cikin al’umma, maimakon haka su taimaka musu su daina wannan dabi’a.
Ta yi wannan kiran ne a Abeokuta bayan an yi mata nadi a matsayin babbar jakadiyar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi (WADA), wanda hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA), reshen jihar Ogun ta yi mata.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Misis Abiodun ta ce har yanzu wadanda aka yi fama da su wajen ta’ammali da miyagun kwayoyi za su kasance masu amfani ga al’ummarsu idan mutane suka rungume su.
Karanta kuma: Shaye-shayen Muggan Kwayoyi Ne, Ke Rura Kashe-Kashe A Najeriya—– NAPTIP
Ta danganta yawaitar shaye-shayen miyagun kwayoyi da yanayin tattalin arziki da ya kamata daidaikun mutane su sarrafa su yadda ya kamata.
Uwargidan Gwamnan ta bayar da shawarar dagewa da bin diddigin yadda mutane ke mayar da martani ga al’amuran da ba su ji dadi ba, domin bai kamata matasa su rika yin shaye-shaye a matsayin kayan aikin jin dadin jama’a ba ballantana ya zama abin kwantar da hankali ga matsalolin zamantakewa, musamman a yara daga gidajen da suka lalace.
Ta kuma jaddada bukatar wayar da kai na yaki da wannan barazana daga kowa, inda ta yi alkawarin bayar da goyon bayanta ga hukumar NDLEA da sauran ’yan uwa mata, domin dakile ta’ammali da miyagun kwayoyi.
Jaridar Daily Trust ta rawaito, Tun da farko a nata jawabin, sabon Kwamandan NDLEA, Ibinabo Archie-Abia, ta ce ya zama wajibi a dakile yawaitar shan miyagun kwayoyi a kasar nan, inda ta kara da cewa hada karfi da karfe zai zama maganin wannan yanayi mara dadi.
A wani labarin kuma: FG Ta Sami Naira Biliyan 600 Daga Harajin VAT a Watanni 8
Hukumar Kididdiga ta Kasa, NBS, ta ce adadin kudin harajin da aka samu daga harajin VAT, ya kai Naira biliyan 600.15 a watanni 8 na shekarar 2022.
Hakan ya zo ne bisa ga rahoton VAT Q2 2022 da aka fitar a Abuja ranar Asabar.