By Abbas Yakubu Yaura
Tsohuwar Uwargidan Gwamnan Jihar Filato, kuma Uwargidan marigayi Cif Solomon Lar, Farfesa Mary Lar, ta yaba da fitowar Dakta Iyorchia Ayu a matsayin sabon shugaban jam’iyyar PDP na kasa, inda ta bayyana shi a matsayin “Dan ga Uba na gaskiya”.
Lar ta bayyana haka ne a Abuja ranar Alhamis lokacin da shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP Walid Jibrin da kuma sabon shugabanta na kasa Dakta Ayu suka jagoranci BoT da kwamitin ayyuka na kasa suka kai mata ziyarar ban girma.
Wannan dai na zuwa ne a wata sanarwa da shugaban jam’iyyar PDP na kasa ya sanyawa hannu mai taken ‘Bazawarar Lar, Mary, ta yaba da fitowar Ayu a matsayin Shugaban PDP, tana addu’ar samun nasara ga jam’iyar PDP.
Mary Lar wadda ita ce matar marigayi Solomon Lar – shugaban jam’iyyar PDP na kasa na farko – ta bayyana jin dadin ta da yadda sabbin shugabannin jam’iyyar suka ga sun cancanci tunawa da ita, ta kuma yi addu’ar Allah ya albarkaci aikinta da kuma burinta na siyasa.
Tace, “Na gode da zuwan mu, dangin marigayi Chief Solomon Lar. Mun dauka an manta da mu, an bar mu.Da muka yi tunanin abin ya wuce, sai ga Allah cikin ikonsa ya tada wani dansa ya zauna a kan kujerarsa. Kai dan ne ga uba na gaskiya.
A cewarsa, “Babanmu, Marigayi Solomon Lar, ya shuka hadaya mai rai. Ee, sadaukarwa ce mai rai. Kuma shi ya sa a yau dansa, Dokta Iyorchia Ayu, ke zaune a kan kujerar daya zauna a kai.”
Tun da farko shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Dakta Ayu, da kuma shugaban kwamitin amintattu na PDP, Walid Jibrin, sun bayyana cewa sun je gidan ne domin tunawa da babban jigo da kuma tabbatar wa ‘yan uwa cewa jam’iyyar haƙiƙa Nijeriya, har yanzu tana tunawa da shi da kuma babban hidima ga Ƙasar.