Matar mawaki Davido Adeleke, wato Chioma Avril Roland ta warke daga cutar Koronabairos kwanaki 23 da cutar ta kamata.
Davido ya tabbatar da hakann ne a shafinsa nna Twitter, a ranar Lahadin 19 ga watan Afrilunn 2020. Inda ya ce an sake yiwa Chioma gwaji har sau biyu inda kuma ba a same ta da cutar ba.
Davido ya godewa Allah da saukin da matarsa ta samu, inda ya yi godiya bisa addu’o’in da al’umma suka taya shi. “na ji dadi, ina sonku baki daya.” Inji shi.
A ranar Juma’ar 27 ga watan Maris, Davido ya rubuta a shafinsa na Instagram yana bayyana cewa Koronabairos ta kama matarsa.