Matar Obiano ta cancanta tasha Mari a wajen Bianca Ojukwu — Cewar Hadimin Gwamnan Lagos
Mai ba Gwamnan Jahar Lagos Shawara na Musamman akan Albarkatun Ruwa da Magudanan Ruwa Joe Igbokwe yace Uwargidan Gwamnan Jahar Anambra mai sauka Ebelechukwu Obiano “ta samu abinda take so” a faɗan ta Bianca Ojukwu, Matar Marigayi Chukwuemeka Odumegwu-Ojukwu.
Bayan an rantsar da Charles Soludo a matsayin Sabon Gwamnan Jahar Anambra a ranar Alhamis da safe, Ebelechukwu Obiano taje inda Bianca take zaune, wanda daganan suka cigaba da faɗa, wannan mummunan lamari ya janyo hankulan Jami’an tsaro da wasu manyan mutane, wanda suka cire Matar Obiano daga jikin Bianca.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-Yanzu: Bas dauke da yan gudun hijira daga Ukraine ta kife a Lithuania
“Dubi irin wannan kunya. Matar Obiano taje ta tunkara tare da cin mutuncin Bianca Ojukwu, sai ta samu abinda ya kamata ta samu. Babban Darasi ga Kowa,” Inji Igbokwe, Ɗan Asalin garin Nnewi ta Jahar Anambra, ya rubuta a shafin sa na Facebook, tare da bidiyo akan abinda ya faru.
Haka zalika, Gwamna Soludo ya nemi yafiyar Al’ummar Anambra, Abokai, da baƙi da suka halarci taron rantsar dashi, da irin abinda ya faru a lokacin bikin rantsar dashi.
A cikin wata sanarwa da Mai Taimaka Ma Soludo ta fuskar Yaɗa Labaru, Joe Anatune, yace hakan ya faru ne a dalilin rashin dangantaka daya faru a tsakanin su, wanda hakan ya haddasa rikicin, inji sanarwar