Wata matar aure ta zama abin magana a yanar gizo, saboda ta raka mijinta wajen aikin sa na aikin famfo.
Matar auren ta sanya bidiyon ne a manhajar TikTok domin nuna lokacin da, ita da mijinta suka yi wani aikin kwangila tare. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
Sun yi aiki tare inda suka kammala kwangilar cikin lokaci. Kwangilar da suka yi ta ƙunshi sanya babban tankin sama.
KU KARANTA KUMA: Bidiyon Wata Mai Siyar Da Sababbin Kuɗin Naira Ya Janyo Cece-Kuce
Bayan wannan kuma, sun shimfiɗa bututun ruwa daga wajen da ruwan yake zuwa wurare daban-daban a cikin ginin.
A cewar ta sun gudanar da aikin ne a wani babban ɗakin taro na cocin Jehovah Witness kingdom. Matar auren itace ta sama yayin da mijinta ya tsaya a ƙasa.
Can daga baya sai mijinta ya hau sama domin taimaka mata lokacin da za a ɗaga tankin domin a sanya shi.
Wannan alaƙar mai kyau dake a tsakanin ma’auratan biyu ta burge mutane da dama.
Wani shafi mai amfani da sunan @rencoplumbing, shine ya sanya bidiyon a manhajar TikTok.
Ku kalli bidiyon a nan.
Bidiyon Wata Budurwa Mai Aski Da Falleliyar Wuƙa Ya Ɗauki Hankula
A wani labarin na daban kuma, wata budurwa ta zo da wani salo na ban mamaki, inda take aski da falleliyar wuƙa.
Wata budurwa mai yin aski ta karaɗe yanar gizo bayan bidiyon ta ya bayyana inda take yiwa wani aski da wuƙa.
Budurwar mai suna Lydia Williams ta sanya wani bidiyo a TikTok, wanda ya nuna yadda tayi amfani da wuƙar cikin ƙwarewa ta yiwa wani matashin yaro aski.
A cikin bidiyon wanda yanzu haka sama da mutum dubu ɗari da hamsin suka kalle sa, yaron ya zauna yana jiran Lydia ta wasa wuƙarta.