Mai dakin tsohon shugaban hukumar ‘yan sanda na kasa Mista Misiliu Smith, Hajia Ariat Smith ta rasu tana da shekaru 65 a duniya.
An bayyana labarin rasuwar nata da yammacin ranar Juma’a, sai dai ba bayyana dalilin rasuwar tata ba.
A cikin wata takarda da sakataren shugaban yada labaran gwamnatin jihar Legas ya fitar Mista Gboyega Akosile ya sanyawa hannu, yace za a yi jana’izarta kamar yadda addinin musulunci ya tanadar.
https://dimokuradiyya.com.ng/dokar-hana-fita-yan-sanda-sun-cafke-mutum-325-a-legas/
Gwamnatin jihar Legas ta jajantawa iyalan tsohon shugaban hukumar ‘yan sandan na kasa bisa babban rashin da aka musu.
Mai mutuwar ta mutu ta bar Mai gidanta Musiliu A. K. Smith, sai ‘ya’yan cikinta da suka hada da Mista Mujeed Adekunle Smith da Misis Atiat Olubunmi Sheidu.
Idan ba a manta ba Mista Smith an nada shugaban hukumar ‘yan sanda na kasa a Mayun shekara ta 1999 sannan ya yu ritaya a watan Maris din shekara ta 2002