Misis Mary Abiola Wayas, matar tsohon shugaban majalisar dattawa, Marigayi Joseph Wayas, ta rasu kwanaki 12 kacal bayan mijinta ya rasu a wani asibiti dake Birnin Landan.
Marigayi Misis Wayas ya mutu a Burtaniya a ranar 30 ga Nuwamban shekarar, 2021.
Yayin da Mai dakin sa ta mutu a wani Asibitin Landan a ranar 12 ga Disamba 2021, bayan gajeriyar rashin lafiya, kamar yadda Dan Joseph Wayas ya bayyana.
Ta rasu ta bar ‘ya’ya biyar, jikoki da dama