Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ya ce akwai gudummawar da matasa za su bayar wajen dakile yaduwar cutar korona. Shugaban ya jaddada cewa; ya kamata matasa su yi bakin ƙoƙarinsu wurin daƙile yaɗuwar cutar korona.
Dakta Tedros Adhanom Ghebreyesus ya yi wannan roƙon ne a wani jawabi da ya yi a ranar matasa ta duniya. Tedros ya ce; “duk da cewa matasa ba sa cikin hatsarin kamuwa da cutar sosai, za su taka rawa sosai wurin yaƙi da ita,” kamar yadda Bbc Hausa ta labarto.
Amurka da Nahiyar Turai na fuskantar ƙaruwar cutar a tsakanin matasa a ‘yan watannin nan. Ana alaƙanta hakan da janye ko sassauta dokar kulle.