Wani matashi a kauyen Ogidi dake karamar hukumar Idemili na Jihar Anambra, ya shiga hannun matasayan uwan shi a kauyen, bayan da ya lakada wa mahaifiyar sa duka.
An ga matashin Cikin wani faifan bidiyo mai kusan mintuna biyu yana lakadawa tsohuwar tashi duka da wani jibgegen sanda, kana yana tattake ta da kafa.
Kazalika a wani bangaren bidiyon an ga yadda matashin ke ajiye sandar yana sharara mata mari da naushi har ma da tattaka ta da kafa yana shure ta, bayan da ya janyo ta zuwa wani lungu da ba lallai a iya ganin shi ba sakamakon yanayin yara ne da mata jibge a lungun.
To kuma bayan da bidiyon ya bazu a shafukan sada zumunta na zamani ne har ya kai ga idanun matasan kauyen, suka bazama neman sa ruwa a jallo har suka gano shi, suka ajiye shi bainar jama’a suka bashi kashi.
Ko da yake matashin mai suna Maduegbunam ya amsa laifin sa, amma hakan bai hana matasan daure shi a jikin bishiya su zane shi ba kamar yadda al’adar su ta ba su dama, domin hakan zai zama izna ga yan baya.
Kawo yanzu dai babu wata hujja da matashin ya fitar ta lakadawa wa dattijuwar mahaifiyar tasa, amma sau da dama ana samun matsaloli irin wannan dake da alaka da shaye-shaye.