Matasan Arewa ƙarƙashin Majalisar Matasa ta Arewa sun yabawa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari akan naɗa Mohammed Bello-Koko a matsayin sabon Manaja-Darakta na Hukumar Kula da Tashoshin Ruwa.
Ƙungiyar ta ƙunshi matasa da suka futo daga Jahohi goma 19 na yankin Arewa da Abuja.
Matasan a sanarwar da suka fitar mai sa hannun Kakakin ta Mohammed Ɗanlami aka rarraba wa Manema Labaru a Kaduna a ranar Laraba, sun yi kira ga sabon Shugaban Hukumar kula da Tashoshin Ruwa da ya ɗauki sabon damar da ya samu wajen inganta ɓangaren ruwa da Tattalin Arzikin Najeriya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Magoya bayan Aregbesola na zanga-zanga a hedkwatar ‘yan sandan Osun, sun bukaci a tsige Kwamishina
A lokacin da suke taya shi murna akan naɗa shi da akayi, Ƙungiyar tayi kira ga Ma’aikata da Shuwagabancin Hukumar ta NPA dasu baiwa sabon Manaja-Darakta dukkanin goyon bayan daya ke buƙata domin samun nasara a mulkin sa.
Sanarwar tace kamar haka “Majalisar Matasa Arewa ta hanyar Shugabancin ta, tana taya Mohammed Bello-Koko murna akan naɗa shi da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari yayi a matsayin sabon Manaja-Darakta na Hukamar Kula da Tashoshin Ruwa.
Koko dai ya kasance muƙaddashin Manaja-Darakta, biyo bayan dakatar da Hadiza Bala Usman daga ofishin ta, wanda Shugaban Ƙasa yayi a shekarar 2021.