Gabanin zaben fidda gwani na yan takarar shugaban kasa a jam’iyyar (APC), wasu gungun matasa yau a jihar Gombe, sun fito kan tituna domin nuna goyon bayansu ga Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi.
Matasan da suka fito dandazo guda an gansu suna rawa da tattaki daga filin Doma da ke kan titin Biu zuwa dandalin APC a cikin babban birnin Gombe.
Tafiyar da matasan suka yi ta kai nisan kilomita 7.5, kuma wasu daga cikin matasan sun tabbatar da cewa sun fara wannan tattakin ne domin nuna goyon baya ga Gwamna Bello.
A cewar su, domin ya tabbatar da cewa shi ne matashin dan siyasa daya tilo da ya damu da matasan Najeriya.
A cewar Usman Soja, Ko’odinetan Kungiyar Tallafawa Yahaya Bello a Gombe, Gwamnan Jihar Kogi ne kadai dan takara da ke da kwarewar jagoranci.
Shima da yake magana, Nasiru Baba ya bayyana cewa matasan sun yi takaicin shekaru da shekaru na shugabannin da suka shude.
“Mu dai muna son Yahaya Bello ne ya zama shugabanmu na gaba, saboda muna ta kokarin tsofaffi da dattawa kuma babu abin da ya canza a rayuwar matasa.
Don haka a matsayinmu na matasa muna bukatar Yahaya Bello wanda namu ne ya canza mana kamanni,” inji su.
Comments 1